KUNGIYAR SBU VANGUARD TA KARBI BAKUNCIN JIGA-JIGAN APC DAGA NINGI

Daga: Abubakar Musa 

Kungiyar SBU Vanguard mai marawa kudirin takarar Sanata Shehu Buba Umar baya a shekarar 2027, ta karɓi bakuncin manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da kuma shugabannin SBU daga ƙaramar hukumar Ningi.

Taron ya gudana a hedkotan SBU Vanguard dake cikin garin Bauchi karkashin jagorancin Engr. Ishaq Dabo (Darman Toro). Wannan Kungiya tayi fice wajen tallatan alherin Sanata Shehu Buba Umar a fadin Jahar Bauchi. 

Tsohon ɗan Majalisar Tarayya da ya wakilci mazabar Ningi/Warji, Hon. Baba Iyali, tare da wasu fitattun ‘yan siyasa na APC daga Ningi, sun kai ziyara ofishin SBU Vanguard da ke jihar Bauchi, inda suka gana da manyan jagororin tafiyar siyasar Sanata Shehu Buba.

A yayin taron, an tabbatar da kulla haɗin kai da amana tsakanin bangarorin domin ƙarfafa tafiyar neman kujerar gwamnan jihar Bauchi da Sanata Shehu Buba ke yi a zaben 2027.

Wannan taro ya ci gaba da jawo hazikan matasa, shugabannin al’umma da masu kishin cigaban Bauchi domin marawa wannan kuduri baya. An gudanar da zaman ne ƙarƙashin jagorancin Engr. Ishaq Dabo, daya daga cikin manyan masu ruwa da tsaki a tafiyar.

Cigaba da hulda da matasa, mata da kuma manyan masu ruka da saki a fadin jahar na kara fadada aniyar Sanata Shehu Buba Umar na zaman gomnan Jahar Bauchi a zabe mai zuwa. 


Comments

Popular posts from this blog

Youths Assembly of Nigeria Recognizes Dr. Abdulkarim's Philanthropy with Top Award

Bodejo’s Arrest: AGGA Warns APC Risks Losing the North Ahead of 2027

Gombe Motorcycle Ban: ACYLF Speaks